Jami´an shiga tsakani a rigingimmun Afrika sun buɗa taro a Zannibar | Labarai | DW | 24.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami´an shiga tsakani a rigingimmun Afrika sun buɗa taro a Zannibar

Manya-manyan jami´an shiga tsakani, a rikita-rikitar da ke wakana a sassa daban-daban na Afrika,sun buɗa wani maihimmin taro, a tsibirin Zanzibar na ƙasat Tanzania, bisa gayyatar hukumar ƙasar Suizland mai kula da bunƙasar cuɗe ni in cuɗe ka, tsakanin al´ummomin dunia, da kuma gwamnatin ƙasar Nowe.

A tsawan kawanaki 3, mahalarta taron, za su gudanar da mahaurori, agame da tashe- tashen hankulla da ke ci gaba da ɗaiɗaita nahiyar Afrika.

Su na kyauatata zaton ɓullo da wani saban sallo na riga kafi, da ɓarkewar rikici a Afrika, da kuma mattakan warware shi, idan ya abku.