Jamian Iraqi sunce sun kame tare da sakin Zarkawi bisa kuskure | Labarai | DW | 16.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamian Iraqi sunce sun kame tare da sakin Zarkawi bisa kuskure

Mataimakin ministan harkokin cikin gida na Iraqi,ya baiyana cewa yan sandan kasar sun cafke tare da kuma sake Abu Mus’ab Al zarkawai bisa kuskure a shekarar da ta gabata.

Hussein Kamal ya fadawa manema labarai cewa,an tsare Zarkawi ne a garin Falluja,amma daga bisani aka sake shi don babu wanda ya gane shi.

Wani jamin Amurka yace jamian leken asiri na Amurkan sunyi imanin cewa,wannan zance bai kama ruwa ba.

Ana dai zargin Zarkawi, mutumin da ake nema ruwa a jallo,da laifukan hare haren bam,kissan kai da sare kan yan kasashen waje.

Dakarun Amurka sunce a farkon wannan shekara ne suka yi daf da kama Al zarkawi.