1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami´an hukumar IAEA sun isa Iran

Sifetocin hukumar kula da makamashin nukiliya ta MDD sun isa kasar Iran don kai ziyara a tashoshin sarrafa sinadarin uranium na kasar. Shugaban hukumar ta IAEA Mohammed El-Baradei wanda ake sa ran isar sa Iran a gobe lahadi, zai yi kokarin shawo kan shugabannin kasar mai bin tsarin Islama don su kara ba da hadin kai. Kwamitin sulhu na MDD na bukatar Iran ta dakatar da dukkan aikace aikace na samar da karafan uranium kafin karshen wannan wata na afrilu. Gwamnatin Teheran dai na fuskantar barazana kakkaba mata takunkumi idan ta ki ba da kai ga bukatun kwamitin sulhu.