Jamian diplomasiya na yamma da kuma na Afrika zasu tattauna makomar Somalia | Labarai | DW | 19.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamian diplomasiya na yamma da kuma na Afrika zasu tattauna makomar Somalia

Jamian diplomasiya na kasashen yamma dana Afrika sun hallara a birnin Nairobi na kasar Kenya,a kokarinsu na ganin an samarda tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin rikon kwarya ta Somalia da kuma shugabanin kotunan islama.

Jamian diplomasiya na kasashen dake halartar taron wadanda suka hada da Amurka,kasashen turai,majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar kasashen larabawa,sunce zasuyi kokarin ganin cewa bangarorin biyu sun aiwatar da yarjeniyoyi da suka amince a aki tun baya.

Hakazalika zasu gana da dukkanisu bangarorin biyu a lokuta daban daban don tabbatar da cewa sun sadaukar ta kawunansu ga taron da aka shirya zaa gudanar ranar 30 ga watan oktoba.