Jami´an bayar da agaji sun fara janyewa daga gabashin Chad | Labarai | DW | 03.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami´an bayar da agaji sun fara janyewa daga gabashin Chad

Hukumomin Mdd da kuma wasu kungiyoyin sa kai sun fara janye jami´an su daga gabashin kasar Chad.

Daukar wannan mataki a cewar rahotanni na da nasaba da irin ayyukan yan tawaye dake ci gaba da tsananta a wannan yanki.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ya rawaito jami´an bayar da agajin gaggawar na cewa yan tawayen, a yanzu haka sun yiwa garin Guereda sansani, bayan da´a ranar lahadi suka kaiwa dakarun gwamnati hari.

Rahotanni dai sun nunar da cewa fara janyewar jami´an bayar da agajin, a yanzu haka ya fara haifar da rashin jami´ai da zasu kula da matsugunan yan gudun hijira.

Matsugunan yan gudun hijirar da Mdd ke kula dashi, a yanzu haka na a amatsayin masaukin yan gudun hijira ne daga Sudan kusan dubu dari biyu.