1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'a mafi girma a Nahiyar Afirka

Abba BashirOctober 10, 2005

Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria

https://p.dw.com/p/BwXL
Dalibai a Jami'a
Dalibai a Jami'aHoto: AP

Masu sauraron mu barkammu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya : fatawar mu ta wannan makon ta fito daga hanun Muntaka Abdul-Hadi Dabo, mazauni a birnin Kano dake tarayar Nigeria,mai sauraron namu yace gaisuwa da fatan kuna lafiya,Allah ya sa haka amin. Wai shin a duk fadin nahiyar mu ta Africa wace Jami’a(University) ce ta fi girma,kuma tana da yawan dalibai nawa ne?

Amsa:Idan ana magana game da jami’ar data fi kowace girma a nahiyar Africa, sai mu ce Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria dake tarayar Nigeria ita ce mafi girma a duk nahiyar Africa.Domin a halin yanzu wanan jami’a nada yawan dalibai da suka tasama 35,000 da kuma babar haraba,sai kuma wasu kananan asibitoci na koyarwa dake karkashinta,banda ma wasu cibiyoyin bincike dake kusa da harabar jami’ar ta Ahmadu Bello ta Zaria dake arewacin Nigeria.

A shekarar data gabata jami’ar Ahmadu Bello ta zaria ta sami taimakon har na dola miliyan daya daga gwamnatin taraya,don kafa sashin na’ura mai kwakwalwa na Computer da kuma hanyoyin shiga yanar giza gizo wato Internet,tun daga wanan lokacin ne aka kafa wani kwamiti na jami’ar da zai tabatar da ganin wanan shirin ya fara aiki ka’in da na’in.

Bugu da kari jami’ar ta Ahmadu Bello ta Zaria nada hadin kai da kasahe da dama na duniya a fannin ilimi.

A lokacin da turawan mulkin malakar yammacin turai suka gudanar da salo irin na mulkin mallaka,sun kafa jami’o’i da kuma cibiyoyin bincike da dama,to sai dai kuma irin wadanan jami’o’i ko cibiyoyin bincike sun durkushe a sabili da dalilai na tabarbarewar tattalin arziki,wannan dalili ne ya sanya babban masani a fannin ilimin kimiyya dan asalin kasar Ivory Coast Hariss Memel-Fote ya gabatar da wata shawara ta kafa cibiyar nazarin kimiya da aladun alumar Africa da taimakon gwamnatin Ivory Coast.

Ko wane irin dalili ne ya sanya ake da karancin jami’o’i a Africa,koda yake akwai jami’o’in da suka yi fice a kasashe kamar su Africa ta kudu,Nigeria,Ghana,Kenya Senel,Madagaskar,Uganda,

har zuwa kasar masar da Morocco?

A ta bakin shehun malamin na kasar Ivory Coast Mamel Pote,ba wai matsaloli na rashin isassun kudade na tafiyar da jami’o’i ne babbar matsalar da ake fuskan ta a nahiyar Africa ba,a’a matsaloli na siyasa da al’adu suma na taka muhimiyar rawa wajen kafa jami’i’o masu inganci a nahiyar ta Africa.

A game da samar da jami’oi masu inganci da kuma cibiyoyin ilimi a duniya baki daya ne,ya sanya kwararu daga kasahe 51 da suka hada da kasahen Senegal,Benin,jamhuriyar democradiyar Congo nahiyar Africa da kuma wakilan kasahen Faransa,Italiya Swizerland da Japan zasu gudanar da wani baban taron su,don yin nazari kan yadda za’a bunkasa ilimi a jami’o’i da kuma manyan tsangayoyi na fannin ilimi.

Da fatan mai sauraron namu ya gamsu.