1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Nijar ta samu ci-gaban rayuwar al'umma

Gazali Abdou Tasawa MAB
March 14, 2024

Hukumar Raya Kasashe ta MDD wato UNDP ta nunar da cewa Nijar ta samu ci- gaban rayuwar dan Adam tare da daina zama koma-bayan kasashe. Wannan shi ne karon farko a cikin shekaru 10 da ta tsere wa kasashe hudu na duniya.

https://p.dw.com/p/4dWYK
'Yan Nijar sun fita daga sahun kutal a fannin ci-gaba
'Yan Nijar sun fita daga sahun kutal a fannin ci-gabaHoto: DW

Shekaru da dama rahoton shekara-shekara na Hukumar Raya Kasashe ta MDD wato PNUD ko UNDP ya shafe yana bayyana Nijar a matsayin ta karshe ko kusa da ta karshe a fannin ci-gaban yanayin rayuwar dan'Adam a Duniya. Sai dai rahoton  2023-2024 ya bayyana cewa Nijar ta daina zama koma-bayan kasashe, inda ta zo ta 189 kuma ta yi kunnen doki da Chadi amma ta tsere wa kasashe uku ciki har da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Soudan ta Kudu da Somaliya.

Rabuwar kai kan dalilin ci-gaban da Nijar ta samu

Fannin kiwo lafiyar mata na daga cikin fannonin da aka samu ci-gaba a Nijar
Fannin kiwo lafiyar mata na daga cikin fannonin da aka samu ci-gaba a NijarHoto: Nicolas RemeneAFP/Getty Images

Wasu ‘yan Nijar na danganta wannan ci-gaba da kasar ta samu a fannin yanayin rayuwar dan'Adam da abin da suka kira tuballan ci- gaba da gwamnatin Mohamed Bazoum ta dora kafin sojoji su kifar da ita. Soule Oumarou na kungiyar FCR na daga cikin masu wannan ra'ayi. Amma Mahamadou Ismael, wani dan fafutika da ke goyon bayan mulkin sojan Nijar na ganin cewar ci gaban da aka samu abun a yaba ne, amma akwai yiwuwar wani makirci ne da kasashen Yamma ke son shiryawa ga Nijar.

Hukumomin Nijar ba su ce uffan ba tukuna

Har yanzu fannin ilimin kananan yara na bukatar kulawa a Jamhuriyar Nijar
Har yanzu fannin ilimin kananan yara na bukatar kulawa a Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou/DW

Kokarin da DW ta yi donjin ta bakin hukumar kididdiga ta kasa kan wannan ci gaba da hukumar UNDP ta ce Nijar ta samu ya ci tura, inda babban daraktan ma'aikatar ya ce kawo yanzu ba za su yi wani tsokaci a kai ba har sai bayan sun yi bitar bayanan da rahoton ya kunsa. Sai dai kasar ta Nijar ta yi kaurin suna wajen zama kutal a duniya a shekarun baya.