Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango: Rasa matsuguni
Fiye da mutane 200,000 suka warwatse a sansanonin ''yan gudun hijira 17 a yankunan garin Kalemie na gabashin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango. Yanayi mai wuya amma hafa yafi zama a gida.
Yamma a sansanin 'yan gudun hijira
Yara biyu da yamma a sansanin 'yan gudun hijira na Kalenge. Dubban mutane suka tsere daga gidaje sakamakon tashin hankali a lardin Tanganyika na gabashin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango. Yanzu galibi suna rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijira da ke kewayen Kalemie. A ciki akwai yaran wadanda rikicin ya raba da iyaye.
Wuta a gidaje
'Yan gudun hijira na Kalenge suna rayuwa a bukka na kara. Ana yawan samun gobara da ke saurin yaduwa daga gida zuwa gida. Haka lamarin yake a sauran sansanonin da ke yankin. A watan Yuni kadai an samu gobara kusan duk sansanonin. Sannan a watan Agusta rabin sansanin Kakinga ya kone kurmus tare da rasa ran yaro karami.
Makaranta ta zama sansani
Wannan yara suna makarantar primari ta Filtsaf a Kalemie, amma ba domin koyon karatu ba. Sun tsere daga Tabacongo sakamakon rikici a watan Mayu. Wasu na fama da cutuka da yunwa.
Cuta a jini
Ma'aikatan kungiyar lafiya na gari na kowa suna kwajin cutar zazzabin cizon sauro a wannan asibin sha-ka tafi. Kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na wadanda ke sansanin 'yan gudun hijira na Kalunga suna dauke da zazzabin cizon sauro. Sannan likitocin suna maganin cutar yunwa da kyanda.
Iyalai sun tsere
"Yaranmu da tsaffi na mutuwa" a cewar Kisompo Selemani (A hoto: na biyu daga hagu). Shugaban Twa yana tare da matarsa da yara hudu a Kilunga tun wtaan Nowamba. Iyalan sun tsere lokacin da aka kai hari a Twa kuma dattijon dan shekara 64 ya bukaci gwamnati ta yi wani abu.
Babu ilimi
A gaba daya babu makarantu a sansani, ko wajen da yara za su sakata.
Neman hanyar rayuwa
Wata mata tana sayar da taba, da ashana, tare da yara a sansanin Kilunga. Galibin 'yan gudun hijira suna samun abinci sau daya ne a rana.
Neman ruwa mai tsafta
Yayin da yara ke filin kwallo na Mukuku, mata suna neman ruwa. Akwai rashin ruwa mai tsafta. Wannan na kara samun cutuka masu yaduwa kamar amai da gudawa wanda ake samu ta ruwan da ya gurbata.
Neman aiki
Zaman lafiyar yankin na tangal-tangal. 'yan gudun hijira da dama na neman kariya a Kalemie. Domin samun kudi, suna aiki a kauyukan da ke yankin ko tattaro itacen girki.
Wajen zama na wucin gadi?
Rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira babu sauki. Sai dai haka yafi ga mutane da dama. Galibi sun yi shaida na tashin hankali da ya saka suka tsere. Kungiyarlikitoci na gari na kowa ta ce akwai wadanda suke bukatar duba lafiyar kwakwalwa.
Sauro ya zama gagarumin barazana
A sansanin Kalonda, 'yar shekaru 69 Kabeja Kanusiki tana kula da jikokinta marasa lafiya. Gidan sauro da take da shi ya dace ya kare su daga zazzabi. A gaba daya akwai 'yan gudun hijira kimanin 210,000 suke rayuwa a sansanonin na kewayen Kalemie.