Tsohon Firaminista Lionel Zinsou da Patrice Talon, za su fafata a zagaye na biyu na zaben da za a yi a ranar 20 ga watan nan na Maris bayan da dukkaninsu suka gaza samun kashi hamsin cikin dari.
https://p.dw.com/p/1IAPC
Talla
Ana dai kallon shugaba Thomas Boni Yayi a matsayin dattijo bayan da yaki neman tazarce bayan kammala wa'adi na biyu sabanin wasu shugabannin Afirka 'yan kama karya.