Jama′ar Iraƙi 120 suke mutuwa kowace rana | Labarai | DW | 10.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jama'ar Iraƙi 120 suke mutuwa kowace rana

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bada rahoton cewa ‘yan Iraƙi kimanin 120 ne suka mutuwa cikin tashe tashen hankula a kowace rana cikin shekaru uku na mamayar da Amurka ta yi wa ƙasar. Hukumar ta faɗi a birnin Geneva jiya Laraba cewa an samu wannan adadi ne bayan binciken haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma gwamnatin Iraƙi. Rahoton ya ƙiyasta cewa aƙalla ‘yan Iraƙi 151,000 aka kashe tsakanin watan Maris na 2003 zuwa watan Yuni na 2006. Rahoton ya ce waɗanda suke rasa rayukan nasu kuma suna tsakanin shekaru 15 zuwa shekaru 59.