Jamaa na tserewa daga Mogadishu | Labarai | DW | 20.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamaa na tserewa daga Mogadishu

Daruruwan mazauna birnin Mogadishu ne suka tsere yau daga cikin birnin biyowa bayan harbe harbe a daren jiya.

Sojin sa kai sun harba rokoki a bangarori daban daban na birnin na Mogadishu inda sojojin Habasha dana Somalian suka maida martani da bindigogin atilare.

Fararen hula 5 suka rasa rayukansu cikinsu har da jariri,wasu kuma 14 suka samu rauni,a arewacin birni inda dakarun AU suka fara jibge kayaiyakin aikinsu.

Wata kungiya da ta kira kanta kungiyar Tauhid da Jihad ta Somalia ta aike da sako ta yanar gizp tana mai daukar alhakin kai wannan hari