Jamíyar Fatah ta amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa | Labarai | DW | 23.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamíyar Fatah ta amince da kafa gwamnatin hadin kan kasa

Jamíyar Fatah ta amince da tayin da Hamas ta yi mata na haɗa hannu domin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa bayan da Fatah ɗin ta sha kaye a watan da ya gabata a zaɓen majalisun dokoki na yankin Palasdinawa. Shugaban Fatah a majalisar dokokin Azzam al-Ahmad yace ko da yake bangarorin biyu na bukatar cimma yarjejeniya a game da wasu tsare tsare, jamíyar Fatah ta amince a bisa manufa domin kafa sabuwar majalisar gudanarwar. Tattaunawar ta zo ne bayan da a hukumance shugaban hukumar gudanarwar Palasdinawan Mahmoud Abbas ya mika takardar bukata ga sabon P/M yankin Palasdinawan Ismaila Haniya ya hanzarta nada sabuwar gwamnati.