1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamíyar Kadima na sami rinjaye a zaben majalisar dokokin Israila

March 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3p

Sabuwar jamíyar Kadima ta mukaddashin P/M Israila Ehud Olmert ita ce a kan gaba da yawan kuriú a zaben majalisun dokoki da aka gudanar. Yayin da a yanzu aka kusa kammala kidaya dukannin kuriún, hukumar zabe ta kasar ta sanar da cewa Jamíyar Kadima ta sami kujeru 28 daga cikin adadin kujeru 120 na adadin yan majalisar dokoki. Jamíyar Labor ita ce ke biye da kujeru 20 yayin da kuma jamíyar Likud wadda ta tade tana jagorantar harkokin siyasa a Israila ta tashi da kujeru 11. A jawabin da ya yi a Hedikwatar jamiyar sa ta Kadima, Ehud Olmert yace a shirye yake ya fara tattaunawa da jamíyun kawance domin kafa gwamnatin hadin gwiwa. Ehud Olmert ya kuma jaddada kudirin sa na shata sabuwar kan iyaka ta kasar Israila tare kuma da gudanar da tattaunawar zaman lafiya da Palasdinawa.