Jakob Zuma: saban shugaban ƙasar Afirka ta Kudu | Siyasa | DW | 04.05.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jakob Zuma: saban shugaban ƙasar Afirka ta Kudu

Ranar shida ga watan Mayu Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu ke tabattar da Jakob Zuma a matsayin saban shugaban ƙasa.Mahimman ƙalubalen da zai fuskanta.

default

Jakob Zuma: Saban shugaban Afirka ta Kudu

Ranar 22 ga watan Afrilu na shekara ta 2009 aka shirya zaɓen ´yan Majalisar Dokoki, zaɓen da jam´iyar ANC ta lashe da gagaramin rinjaye, saboda haka shugabanta Jacob Zuma, ya sami damar zama shugaban ƙasar Afrika ta Kudu baƙar fata na huɗu, tun bayan ƙarshen mulkin wariyar launin fata.

A watan Afrilu na shekara ta 1994 aka shirya zaɓen demokradiya na farko a Afrika ta kudu bayan da ƙasar ta yi fama da mulkin wariyar launin fata.

Jam´iyar ANC ta Nelson Mandela wanda ya share shekaru 27 a kurkuku saboda aƙidarsa ta yaƙi da mulkin wariyar launin fata ta samu babbar nasara.

Shugaba Nelson Mandela, ya sauka daga karagar mulki a watan Juni na shekara ta 1999.

Bayan sabuwar nasara da ta samu a zaɓe ANC ta dora Tabo Mbeki domin maye gurbin Mandela.

Tabon Mbeki yayi tazarce a zaɓe na gaba, to saidai ya cika karo da matsaloli a cikin gudanar da harakokin mulki, inda jam´iyar ANC ta cilasta masa yin murabus a watan Satumba da ya gabata, ta kuma ƙaddamar da Jacob Zuma mai shekaru 67 a duniya a matsayin shugabanta.

Duk da tuhume tuhumen da ya sha fama da su, wanda suka haɗa da cin hanci da rashawa da kuma lalata da ƙananan yara, Jacob Zuma da kotu ta wanke, yayi sa´ar zama shugaban ƙasa baƙar fata na huɗu a Afrika ta Kudu, a sakamakon zaɓen ´yan Majalisun Dokokin da aka shirya ƙasar ,ranar 22 ga watan Afrilun wannan shekara.

Jim kaɗan bayan bayyana sakamakon wannan zaɓe, Zuma dake matsayin shugaba mai jiran gado, ya bayana aniyarsa ta girka gwamnatin haɗin kan ƙasa:

Yanzu lokacin yaƙin neman zaɓe, da lokacin zaɓe sun kau, mun shiga wani saban tafarki na fuskantar alƙawuran da muka yi wa jama´a.

saboda haka,zamu girka gwamnati, wadda zata kula da matsalolin da jama´a ke fama fa su.

Zamu yi aiki da ɓangarori dabam-dabam na al´umar ƙasa, ta hanyar cuɗe ni in cuɗe ka.

A ɓangare yancin jama´a da kuma ƙarfafa tsarin mulkin demokraɗiya saban shugaban ƙasar Afirka ta Kudu ya kwantar da hankalin ´yan siyasa da jama´ar kasa cikin wannan jawabi:

Ba zamu awaitar da komai ba, wanda ya shafi take ´yancin ɗan Adam, kokuma cin zarafin jam´iyun adawa.

Tun shekara ta 1994 aka fara cikkaken zaɓen demokraɗiya a ƙasar Afrika ta Kudu.To saidai ta la´akari da yadda jam´iyar ANC ke wawure kusan dukkan ƙuri´u, babu adawa mai ƙarfi.

Amma a wannan karo, sabuwar jam´iyar COPE da ta ɓalle daga ANC bayan saɓanin da aka samu da tsofan shugaban ƙasa Tabon Mbeki kan iya taka rawar adawa.Wannan shima cigaba ne ga tsarin mulkin demokraɗiya da ya kamata sabuwar gwamnati ta yi amfani da shi, inji tsofan Atbischop Desmond Tutu:

A shekarun farko da muka samun ´yancin kanmu,kuma muka ƙaddamar da tsarin mulkin demokraɗiya, mafi yawan jama´a na zaɓen ANC, amma yanzu al´amurra sun cenza.

Jama´a ta daina zaɗe ido rufe, kowa sai yayi nazarin wanda ya kamata ya shefa ma ƙuri´a, wannan shine demokraɗiya.

Bayan ƙarfafa tsarin mulkin demokraɗiya, ɗaya daga mahimman ƙalubale da shugaba Jacob Zuma ke shirin fuskanta shine yaƙi da cin hanci da rashwa da yayi katutu a wannan ƙasa.

A game da wannan batu dake matsayin annoba yace babu gudu babu ja da baya, to saidai masu adawa da shi na cewa mai bunu a gindi ba shi kishin gobara, domin shi kansa a baya, ya sha fama da zargin aikata wannan mayan lefika, saboda haka a tunanin Marimothu Subamoney ,wani ɗan jarida a Afrika ta kudu tarihin Jacob ta fannin cin hanci ba karamar illa ba ce ga saban matsayinsa na shugaban ƙasa:

Shikansa ba shi iya sa tsari cikin harakokin kuɗinsa.Saboda haka,jama´a da dama ke zargin sa da cin hanci da karɓar rashawa.Ko a baya bayanan nan, kotu ta tuhume da wannan lefi.

Saboda haka a ganina, ba zai iya zama shugaban ƙasa na kwarai ba, kuma su kansu ƙasashen ƙetare ba zasu kalle shi da daraja ba.

Kamar yadda hausawa ke faɗi ra´ayi riga ce a yayin da wasu jama´a ke tunanin cewar Jacob Zuma ba za shi iya jagoranci ba cikin adalci ba,kusan kashi 66 cikin ɗari na jama´ar ƙasa suka kaɗa ƙuri´ar amincewa da jam´iyar ANC ,kuma sun yi imanin cewar Jacob Zuma shine shugaban da ya dace da Afrika ta Kudu a cikin wannan marra.

Kasawa kokuma cimma nasara dai ranar 9 ga watan Mayu ne kotin ƙolin Afrika ta Kudu zata rantsar da Jacob Zuma a matsayin shugaban ƙasa.

Matakin farko shine girka gwamnatin wadda za shi dogaro kanta, domin gudanar da aiyukan da ya alƙawarata a lokacin yaƙin neman zaɓe.

A halin da ake ciki Afrika ta Kudu dake matsayin jagora a Afrika, ta shiga wani hali na kariyar tattalin arziki wanda shine irinsa na farko tun kusan shekaru 20 da suka gabata.

Shekaru 15 bayan zaɓen demokarɗiya na farko,har yanzu kashi 43 cikin ɗari, na al´ummar ƙasa ke rayuwa cikin ƙazamin talauci.

Sannan kashi 40 cikin ɗari na jama´ar ƙasa ke fama da zaman kashe wando.

Wannan matsala ta ƙara muni tsakanin bara da bana, inda kamfanoni da masana´ntu kasar suka soke dubunan ɗarurwan guraben aiki a dalili da rugujewar tattalin arziki da ta zama ruwan dare,kuma da dama daga masu zuba hannayen jari suka daina hada-hada.

Makarantu, asibitoci ruwan sha masu tsafta, da wutar lantarki sai wane da wane.

Bugu da ƙari, Afrika ta Kudu tayi ƙaurin suna ta fannin fashi da makami, sannan itace sahun gaba wajen fama da cutar Sida a duk faɗin duniya.

A game hanyoyin magance duk wannan matsaloli al´umar Afirka ta Kudu ta zuba ido ga Jacob Zuma, domin hausawan kance wai "a dama dawo ta daɗe ga mai jin yinwa".

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita Abdullahi Tanko Bala