Jakadan musamman na MDD ya isa Burma | Labarai | DW | 30.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jakadan musamman na MDD ya isa Burma

Jakadan musamman na MDD Ibrahim Gambari yana a kasar Burma inda zai tattaunawa da jamian mulkin soja na kasar a kokarin kawo karshen tursasawa masu zanga zangar neman kafa demokradiya sukeyi.Rahotanni sunce tataunawar zata gudana ne a hedkwatar mulkin soji ta Naypyidaw kimanin kilomitar 350 daga babban birnin kasar Rangoon inda zanga zangar ke gudana.Cikin mako guda daya wuce dai dakarun kasar sun kai hari guraren ibada na addinin Buddha,inda suka tsare daruruwan malamansu dama wasu masu zanga zangar tare da kuma harbi kann fararen hula.Rahotanni sunce akalla mutane 13 sun rasa rayukansu.Har yanzu kuma ana ci gaba da kwarya kwaryar gangami duk da dokar hana gangami da jamian sojin suka kafa.