Jakadan majalisar dinkin duniya yace bai yi nadama kan kalamansa game da Darfur ba | Labarai | DW | 24.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jakadan majalisar dinkin duniya yace bai yi nadama kan kalamansa game da Darfur ba

Babban jamiin majalisar dinkin duniya da kasar Sudan ta kora Jan Pronk yace ba shi da wata nadama bisa da kalaman da yayi game da halin da ake ciki a yankin darfur wanda ya haddasa korarsa daga kasar ta Sudan.

A jiya litinin ne Pronk ya bar Sudan bayan wasu bayanai da yayi ta hanyar yanar gizo inda yace,rundanar sojin Sudan ta sha kaye har sau biyu a fafatawa da yan tawaye arewacin Darfur,haka kuma basu da wani karfin gwiwa,batu da ya tunzura rundunar sojin kasar wadda ta kira Pronk barazana ga tsaron kasar.

Pronk ya fadawa wani gidan radiyo na kasar Holland cewa babban batu anan shine cewa,an rigaya an rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya a Darfur,amma rundunar sojin kasar ta tana take wannan yarjejeniyar,yace yayi kokarin fallasa su cikin watanni da suka gabata amma hakan baiyi masu dadi ba.