Jakadan Denmark ya bar Syria saboda dalilai na tsaro
February 11, 2006Denmark ta ce jakadanta da sauran ma´aikatan diplomasiyanta a Syria sun bar kasar saboda damuwa da ake da ita ta tsaron lafiyarsu. A makon da ya wuce masu zanga-zangar nuna fushi da buga zanen tozarta Annabi Mohammed SAW da wata jaridar Denmark ta fara yi, sun kona ofishin jakadancin kasar a birnin Damaskus. Ma´aikatar harkokin wajen Denmark ta ce ma´aikatan jakadancinta da aka sake tsugunar da su cikin wani otel, ba sa samun cikakkiyar kariya daga hukumomin Syria. A yau ma dai an ci-gaba da gudanar da zanga-zangar yin tir da cin mutuncin al´umar musulamai. A birnin Potiskum dake cikin jihar Yobe ta tarayyar Nijeriya an yi wata zanga-zangar lumana inda aka kona tutocin wasu kasashen Turai don nuna adawa da wannan batanci ga Manzon Rahma SAW. Wakilin mu a Chadi ma ya rawaito cewar a birnin Ndjamena ma an gudanar da irin wannan zanga-zanga a yau asabar.