1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jaizar Benezir Bhutto

An gudanar da janaizar marigayiya tsohuwar primiyan kasar Pakistan Benezir Bhutto,wadda aka kashe a jiya ayayin da take yakin neman zabe a garin Rawalpindi.Dubbannin yan uwa da abokan arziki sukayi dafifi zuwa kauyen Garhi Khuda Bakhsh,dake kudancin kasar Pakistan,inda nan ne ke zama makabartar Iyalan ta.An dai kwana cikin tashe tashen hankula a sassa daban daban na kasar dangane da nuna bacin rai da wannan kisan gilla da akayiwa shugabar jamiiyyar adawar ta PPP,wadda ta rasa ranta ayayin fafutukan nemarwa alummomin pakistan Democradiyya kamar yadda tasha nunarwa.