Aung San Suu Kyi na iya zarta mukamin shugaban kasa.
November 5, 2015Talla
Wannan zaben dake tafe dai shine irin sa na farko tun lokacin da jagoran kasar ya karbe ragamar mulkin kasar a shekara ta 2011 bayan shafe kusan shekaru 50 kasar na karkashin jagororin mulkin soji.
A yayin da take fadawa manema labarai San Suu Kyi tace zata dara mukamin shugaban kasa muddin suka sami rinjaye a zaben kasar mai cike da tarishi.
A yan kwanakin nan dai jagorar yan adawar kasar Myanmar tasha suka daga bangarori da dama akan gaza tashi tsaye don ganin an kare tsirarun kabilu dake a yankin Rohingya na kasar.