1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran addini a Iran ya ce kasarsa na da ´yancin bunkasa Uranium

October 11, 2006
https://p.dw.com/p/BugE
A daidai lokacin da ake kai ruwa rana da KTA akan gwajin makamin nukiliya da ta ce ta yi, Iran ta sake jaddada cewar ba zata yi watsi da ´yancin ta na amfani da fasahar nukiliya ba. Jagoran addini na jamhuriyar ta Islama, Ayatollah Ali Chameni ya sanar da cewa Teheran ba zata mika kai ga matsin lamba daga kasashen duniya ba kuma zata ci-gaba da aikin inganta sinadarin uranium, duk da wani kudurin MDD wanda ya nema da ta dakatar da aikace aikacen na samar da uranium. Manyan kasashen duniya dai sun yi wa Iran tayin ba ta taimako idan ta yi biyayya da wannan kira. A yau laraba kasashe 5 nan dake da ikon hawa kujerar naki a kwamitin sulhu hade da Jamus zasu koma ga tattaunawa game da takunkumin da za´a dorawa Iran akan shirinta na nukiliya da ake jayayya da ita.