Jagoran adawa a Rasha ya kira gangami
January 28, 2018Talla
Dan siyasar mai shekaru 41 Alexei Navalny ya yi kira ga al'ummar kasar ta Rasha su fito gangamin adawa da mahukuntan da ke shirin zabe kuma su kauracewa zaben da za a yi ranar 18 ga watan Maris duk kuwa da fargabar da ake da ita cewa daga bangaren mahukunta sun shirya kame-kamen 'yan adawar.
A cewar Navalny an tsara gudanar da gangamin a birane sama da 100 ciki har da birnin Moscow da Saint Petersburg inda ake sa ran za a yi taho mu gama tsakanin 'yan adawar masu zanga-zanga da jami'an 'yan sanda.
Jagoran adawar dai Navalny ya bayyana a fefen bidiyo yana cewa sun gaji da shekaru 18 na mulkin danniya da sace-sacen dukiya na masu mulki a kasar ta Rasha a yanzu.