Jadawalin zaɓe a Najeriya | Labarai | DW | 16.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jadawalin zaɓe a Najeriya

Hukumar zaɓe a tarayyar Najeriya ta fitar da sabon jadawalin zaɓe na gaba.

default

Tutar Najeriya

Hukumar zaɓen Nigeria,  ta fitar da jaddawalin zaɓen shugaban ƙasa  na gaba. Hukamar ta INEC, tace imma dai ayi zaɓen a ranar 22 ga watan janairun ko kuma 23 ga watan Aprilun baɗi. Da yake magana shugaban hukumar ta INEC, wato Mauris Iwu, yace sun fidda jadawali kashi biyu ne, kuma hakan sun yi shi ne domin jiran tsammani a bisa abinda majalsar dokokin ƙasar za ta zartar, a kuɗurin tsarin zaɓen ƙasar dake gabanta. Mauris Iwu yace daga nan har izuwa watan Augusta, ko nowamba, idan dai aka basu dokar, to za su iya yin kwaskwarimar da ta kamata. Wannan jadawalin dai ya kumshi zaɓen shugaban ƙasa da 'yan majalisu da gwamnonin jihohi na tarayyar ƙasar. A bisa dokar zaɓen ƙasar da ake anfani da ita a yanzu, to sai watan Aprilun baɗi za ayi zaɓen shugaban ƙasa na gaba, domin maye gurbin shugaba na yanzu wanda wa'adinsa zai ƙare a watan mayun baɗi. Ƙudurin da ke gaban majalisar dokokin ƙasar wanda kuma kwamitin da Mai shari'a Muhammadu Uwaisu ta gabatar, ta buƙaci da ayi zaɓen shugaban ƙasa watanni shidda gabanin rantsarwa, domin baiwa mutanne dake ƙorofi damar su kai ƙara kuma a yanke hukunci, kafin rantsarwa, domin kaucewa giɓen da aka samu bayan zaɓen shugaba 'Yar'adua, inda bayan rantsar da shi har shekaru biyu ana ta kai kawo a kotu. Mawallafi: Usman Shehu Usman Edita: Yahouza Sadissou Madobi