1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jacob Zuma zai fuskanci shari'a

Zulaiha Abubakar
March 16, 2018

Masu gabatar da kara a Afirka ta Kudu sun sanar da cewar tsohon shugaban kasar Jacob Zuma zai fuskanci shari'a a kan laifukan cin hanci da rashawa a loakcin da ya ke rike da madafun iko.

https://p.dw.com/p/2uUGt
Südafrika Präsident Jacob Zuma
Hoto: Getty Images/AFP/R. Jantilal

Babban mai gabatar da kara Shaun Abrahams ya bayyana cewar tsohon shugaban ya jima kasar na zarginsa da manyan laifukan cin amana wadanda hukumar shari'ar kasar ta yi watsi da su a baya lamarin da ya ba shi damar shugabancin kasar,ya kuma kara da cewar daga cikin tsoffin laifukan da aka samu Jacob Zuma da su akwai batun cinikin makamai tun a shekara ta 1990 lokacin da ya ke mataimakan shugaban kasar ko da ya ke a halin yanzu ya karyata wadannan zarge-zarge tare da sukar masu gabatar da karar in da ya kira su da wadanda ba su san aikin su ba.