1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jacob Zuma ya mamaye daukacin jaridun na Jamus

Mohammad Nasiru Awal
February 16, 2018

A wannan makon batun murabus da shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu da jam'iyyarsa ta matsa ya sauka daga karagar mulki, shi ne batun da jaridun Jamus suka yi ta nazari a kansa.

https://p.dw.com/p/2so4q
Südafrikanischer Präsident Jacob Zuma
Hoto: Getty Images/S.Maina

A sharhin da ta rubuta jaridar Neue Zürcher Zeitung ta fara ne da cewa a karshe Shugaba Zuma ya mika wuya da matsin lamba daga jam'iyyarsa ta ANC. Badakalar cin hanci da rashawa, koma bayan tattalin arziki da karancin goyon baya kasa da kashi 20 cikin 100 wadannan duka batutuwa ne da suka yi muni a lokacin mulkin tsohon Shugaba Zuma. Jaridar ta ce an san ‘yan siyasa da yawan saba alkawari, amma na Zuma abin ya yi muni.

Südafrika - neuer Präsident Cyril Ramaphosa – Vereidigung
Hoto: Reuters/M. Hutchings

A lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki a shekarar 2009, Zuma ya yi alkwarin daukar karin matakan yaki da cin hanci musamman a ma'aikatun gwamnati, amma yau shekaru tara baya matsalar ta kara yin muni. Ya kuma yi alkawarin yaki da takauci, amma yanzu yawan talakawa a Afirka ta Kudu ya karu da mutum miliyan hudu.

Ba bu wata yarda da ‘yan siyasa, lamarin da ke barazana ga zaman lafiyar kasar. Za a dauki lokacin mai tsawo kafin a magance wannan illa. Magajin Zuma wato Cyril Ramaphosa yana da babban kalubale na tattalin arziki da zamantakewar jama'a. Babban aikin sabon shugaban na Afirka ta Kudu shi ne ya sake maido da yardar al'ummar kasar ga ‘yan siyasa.

Ita ma a labari da ta buga dangane da sauyin shugabancin a Afirka ta Kudu jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne da cewa ba a da cikakkiyar masaniya a kan rayuwar sabon shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa. Ta ce sabanin Jacob Zuma da aka san kusan komai game da shi har ma sunayen 'ya'yansa 22, amma Ramaphosa mai shekaru 65 kuma shugaban kasar na biyar tun bayan kawon karshen mulkin wariyar launin fata, na tafiyar da rayuwarsa cikin sirri. Jaridar ta kara da cewa Ramaphosa ya karbi ragamar shugabancin kasar cikin mawuyacin hali na karayar tattalin arziki da yawan marasa aikin yi da kuma uwa uba matsalar cin hanci da rashawa.

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland a wannan makon ta leka kasar Mali tana mai cewa shirin zaman lafiyar kasar ya cije.

Mali Präsident Amadou Toumani Toure kehrt zurück
Hoto: Getty Images/AFP/M. Catani

Ta ce yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanya wa hannu a watan Mayun 2015 ta tanadi ba wa gwamnatin tsakiya iko da ilahirin kasar, bayan mamaye arewacin kasar da kawancen Abzinawa da ‘yan aware da masu ikirarin Jihadi suka yi a 2012, amma sojojin Faransa suka fatattake su a farkon 2013. Amma tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar yawan kungiyoyi masu daukar makami sun karu maimakon su ragu.

Da wuya mako guda ya wuce ba a kai hari ba, duk da sojoji da ‘yan sanda dubu 13 na Majalisar Dinkin Duniya da aka girke a yankin. Akwai kuma sojojin Faransa dubu daya a yankin. Rashin hadin kai tsakanin rundunonin na kasa da kasa da takwarorinsu na Mali na daga cikin abubuwan da ke kawo cikas bisa manufar wanzar da zaman lafiya a Mali. Manazarta sun ce akwai bukatar shigar da kowa da kowa a shirin wanzar zaman lafiya matukar ana son a samu biyan bukata.