Jacob Zuma na shirin fuskantar shari′a | Labarai | DW | 29.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jacob Zuma na shirin fuskantar shari'a

Yau aka shirya wata kotu a Afirka ta Kudu za ta bayyana hukuncin a kan ko za ta mayar da tuhume-tuhumen da ake yi wa Shugaba Jacob Zuma da aikata laifuka na cin hanci guda 700 ko akasin haka.

An dai samu Jakob Zuma a shekara ta 2007 da laifin cin hanci,da rashin biyan kuɗaɗen haraji da kuma cinikin makamai na kusan dala biliyan huɗu da rabi tun a lokacin yana shugaban jam'iyyar ANC.Amma a shekara ta 2009 kotun ta janye tuhumar makonnin kadan kafin a zaɓeshi a matsayin shugaban ƙasa.

Saboda a lokacinh lauyoyin Jacob Zuman sun riƙa satar sauraon wayoyin salula tsakanin babban alkalin kotun da kuma wani babban jami'in 'yan sanda na ƙasar,
domin shawo kan kotun don nuna ma ta cewar makirci ne kawai aka shirya wa Zuma abin da ya sa kotu ta yi watsi da tuhume-tuhumen.