Izraela ta kashe palasdinawa biyu a arewacin gaza yau | Labarai | DW | 18.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Izraela ta kashe palasdinawa biyu a arewacin gaza yau

Dakarun Izraela sun kashe larabawan Palasdinu guda biyu ayau a zirin Gaza,yini guda bayan da zauren mdd yayi kira agaresu dasu dakatar da cigaban somame da suke kaiwa yankin cin gashin kann palasdinawan.Su ma kuma a nasu bangaren shugabannin Izraelan,sun bukaci a dakatar da kaiwa kasarsu hare haren rokoki,idan ba haka ba shugabanninsu bazasu sha lafiya ba.Somamen da izraela takai a arewacin Gazan a yau dai ya kashe mutane 2,tare da raunana wasu guda uku inji majiyar asibitocin dake yankin,bayan hare haren kwanaki uku.Wadanda suka rasa rayukansu sun hadar da Hahjuj,mai shekaru 20 da haihuwa da Thaer al-masry mai shekaru 16 da haihuwa.Dakarun Izraelan dai sun hakikance bindige wadannan matsa biyu,a yankin arewacin gazan.Daftarin zaman lafiyan bangarorin biyu daga EU dai na kira da a gudanar da taron kasashen duniya,adangane da wannan hali da bangarorin biyu ke cigaba da kasancewa ciki.