1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Izraela na shrin gina Sabbin gidaje a yankin Palastinawa

Shugaba Mahmoud Abbas na yankin Palastinawa,yayi gargadin cewar Izraela na kokarin gina Ɗaruruwan sabbin gidaje ,a yankunan yahudawa ‚yan kama kama wuri zauna dake gabashin birnin kudus da gaɓar yamma da kogin jordan.Batu da inji shi ya sabawa tattaunawar sulhu da aka koma cigaba dashi a yau.A taron sulhu da Amurka ta ɗauki nauyi a birnin Annapolis a watan daya gabata dai,Izraelan tayi alkawarin bin dukkan ka’idoji da aka gindaya a daftarin samar da zaman lafiyan yankin da aka tsara a 2003.Daga cikin su kuwa har da dakatar da dukkan gine ginen da ake gudanarwa na faɗaɗa yankunan yahudawa ‚yan kama wuri zauna dake yankin na palastinawa.