1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ivory Coast

November 27, 2007
https://p.dw.com/p/CTsP

Shugabannin Ivory Coast sun tattauna batun zaman lafiyar kasar tare da shugaba Blair Campore na Burkina-Faso. Shugaba Laurent Gbabo da Prain-Ministansa Guillaume Soro, suka hallarci taron na birnin Ougadougou da aka kira domin gano bakin zaren warware rikicin kasar. Ana sa ran tattaunawar zata zama wata dama ta sake komawa kann teburin shawara, inda zasu tattauna sauran batutuwan dake kawo rikici tsakannin bangarorin biyu dake gaba da juna. Kasar Ivory Coast ta rabu gida biyu, bayan da ‚yan tawaye suka yi yunkurin kifar da gwamnatin Laurent Gbagbo a shekara ta 2002. Yanzu haka shugaba Gbagbo na shirye-shiryen ziyartar arewacin kasar dake karkashin ikon ‚yan tawaye gobe laraba, domin tabbatarwa al’uma cewar kasar ta shiga wani babi na neman sulhu.