1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya zata jagoranci tawagar kiyaye zaman lafiya a Lebanon...

August 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bum1

Faraministan Italiya, Mr Romano Prodi yace kasar sa a shirye take ta jagoranci tawagar sojin kiyaye zaman lafiya, a kudancin kasar Lebanon.

Mr Prodi, wanda ya shaidawa yan jaridu hakan , ya kara da cewa tuni ya gabatar da wannan bukata, a gaban sakataren Mdd, Mr Kofi Anan.

Kafin dai Italiya ta gabatar da wannan bukata, kafafen yada labaru sun rawaito cewa, Israela ta bukaci kasar ta Italiya data jagoranci wannan tawaga.

A dai karshen makon nan ne ake sa ran babban sakataren Mdd, zai yanke hukunci kann kasar da zata jagoranci tawagar kiyaye zaman lafiyar a kasar ta Lebanon, daga cikin wadanda suka nuna bukatar yin hakan.

A waje daya kuma, dakarun sojin Israela sun shaidar da kisan wasu mambobin kungiyyar Hizboullah guda uku.

Sojin na Israela sun shaidar da aiwatar da wannan aikin ne bayan da akayi wani taho mu gama a tsakanin sojin na Israela da dakarun kungiyyar ta Hizboullah.

Wannan al´amari dai yazo ne mako daya, bayan kawo karshen wannan rikici a tsakanin kungiyyar ta Hizboullah da kuma kasar ta Israela, bisa shiga tsakanin Mdd.