Italiya na nazarin mokoma bayan murabus din Renzi | Labarai | DW | 08.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya na nazarin mokoma bayan murabus din Renzi

Shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella ya soma a wanann Alhamis tattaunawa da bangarorin siyasar kasar domin tsaida matakin da ya dace kasar ta dauka bayan murabus din firaminista Renzi

Shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella ya soma a wanann Alhamis tattaunawa da bangarorin siyasar kasar domin tsaida matakin da ya dace kasar ta dauka tsakanin shirya zaben wucan gadi ko kuma kafa gwamnatin wucin gadi da yi wa kundin tsarin zabe kwaskwarima bayan da shugaban gwamnatin kasar Matteo Renzi ya yi murabus.

Da misalin karfe shida agogon JMT na yammacin jiya Laraba ne firaminista Matteo Renzi ya mika wa shugaban kasar takardar murabus din tasa. Sai dai kuma tsohon firaministan mai shekaru 41 ya ce wannan murabus nasa ba ya nufin karshen makomar siyasarsa ke nan domin a shirye yake ya ci gaba da gwagwarmaya.