1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya: Mutane 37 sun rasu a girgizar kasa

Lateefa Mustapha Ja'afarAugust 24, 2016

Rahotanni daga Italiya na nuni da cewa kawo yanzu sama da mutane 35 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata, sakamakon girgizar kasa.

https://p.dw.com/p/1JoOe
Girgizar kasa a Italiya ta hallaka mutane 37
Girgizar kasa a Italiya ta hallaka mutane 37Hoto: Reuters/E. Grillotti

Acewar hukumar da ke da alhakin kare rayukan fararen hula ta kasar, daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu akwai kananan yara masu yawa. Masu bada agaji na ci gaba da lalube domin ceto sauran wadanda suke da rayukansu, dama wadanda hadarin ya rutsa da su a karkashin gine-gine. Da yake mika sakonsa na jaje da ta'aziyya ga iyalaan wadanda hadarin na girgizar kasar ya rutsa da su, Firaministan Italiyan Matteo Renzi cewa ya yi:

"Ina son in mika sakon jaje da kuma ta'aziyya ga 'yan uwa da iyalan wadanda hadarin ya rutsa dasu. Ga wadanda suka rasa 'ya'yansu a yayin wannan girgizar kasa, ga wadanda suka rasa iyayensu, ga wadanda suka rasa 'yan uwansu da abokansu, ga wadanda ke cikin halin rudu da kuma tashin hankali na rashin sake ganawa da danginsu."

Jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa na fuskantar tarnaki, a kokarin da suke na isa domin yin aikin ceton a yankunan da ke da tsaunuka masu yawa.