Italiya da Kenya sun sanya hannu kan yarjejeniyar sintirin ruwa | Labarai | DW | 30.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya da Kenya sun sanya hannu kan yarjejeniyar sintirin ruwa

Ƙasar Italiya tace ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar sintiri kan teku tsakaninta da ƙasar Libya domin shawo kan matsalar baƙin haure daga nahiyar Afrika zuwa Turai. Ƙarkashin yarjejeniyar da aka sanyawa hannu a birnin Tripoli za a baiwa ƙasar ta Libya aron wasu manyan jiragen ruwa na tsaro guda shida. Ministan harkokin cikin gida na Italiya Giuliano Amato yace dakarun tsaron ƙasashen biyu zasu riƙa yin sintiri ne a bakin iyakokin ruwa na Libya,da yankuna da ake zaton masu fataucin mutane suna anfani da su. A watan da ya gabata kaɗai wasu bakin haure 30 yawancinsu daga ƙasar Masar suka nutse cikin ruwa a kusa da tsibirin Sicily. A kowace shekara kuma dubban yan Afrika da da kuma Asiya suke ƙoƙarin shiga Turai ta kan tekun Mediterranean.