1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila zata ci-gaba da kai farmaki a Zirin Gaza

November 6, 2006
https://p.dw.com/p/BudE
Kungiyoyin Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna wato Hamas da Fatah sun amince da kafa wata gwamnatin hadin kan kasa. Wasu mutane 2 masu magana da yawon kungiyar Hamas ta masu kishin Islama sun ce za´a bayyana sunayen wakilan sabuwar gwamnatin a gun wani taro da za´a yi tsakanin shugaban Falassdinawa Mahmud Abbas da FM Isma´il Haniyeh. A kuma halin da ake ciki Isra´ila ta ce zata ci-gaba da kai farmaki a arewacin Zirin Gaza duk da sukar da take sha daga kasashen duniya. FM Ehud Olmert ya ce burin Isra´ila shine hana Falasdinawa kai harin rokoki cikin Isra´ila. Ya ce ya yi nadama da mutuwar fararen hula a wannan rikici, amma ya zargi kungiyoyin Falasdinawa da amfani da farar hula a matsayin garkuwar dan Adam. Ya zuwa yanzu an kashe Falasdinawa kimanin 50 tun bayan fara wannan farmaki a ranar laraba da ta gabata.