Israila tayi gwajin makami mai kakkabo makami mai linzami irin na Iran | Labarai | DW | 02.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israila tayi gwajin makami mai kakkabo makami mai linzami irin na Iran

A yau jumaa ne kasar Israila tayi gwajin wani makami mai linzami mai tare makamin roket sanfurin kasar Iran.

Wannan gwaji yazo ne kwana guda bayan prime minista Ariel Sharon yayi gargadin cewa kasar Israila ba zata yarda kasar Iran ta mallaki makaman nukiliya ba.

Wannan makami na Israila, ya kakkabo wani makami mai dogon zango mai kama da sanfurin Shahab na kasar Iran,wadda hukumar leken asiri ta Israila MOSAD ta taba baiyana shi da cewa wani babban barazana ne ga tsaron kasar Israilan.

Anyi imanin cewa dai kasar Israila ta mallaki makaman nukiliya kusan 200,kodayake bata amince ko kuma karyata wannan batu ba,haka zalika taki sanya hannu akan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya na kasa da kasa.