Israila ta zartar da daukar tsauraran matakai akan Hamas | Labarai | DW | 19.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israila ta zartar da daukar tsauraran matakai akan Hamas

A yau majalisar zartarwar Israila ta amince da dakatar da mikawa Palasdinawa miliyoyin daloli na kudin haraji da Israilan ke karba a madadin hukumar Palasdinawa. Wannan na a matakin kalubale ga Hamas wadda ta karbi ragamar gudanarwar majalisar dokokin yankin Palasdinawa. Israilan dai na karba kimanin dala miliyan 50 a kowane wata na kudaden harajin kayan da ake shiga da su yankin Palasdinawa. Kudaden nada matukar muhimmanci ga hukumar Palasdinawa domin biyan albashin maáikatan da yawan su ya kai 140,000. Bugu da kari Israilan ta kuma bukaci hukumomi na kasa da kasa da su dakatar da baiwa hukumar Palasdinawan dukkan wani tallafi.