1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta yi watsi da kiran a dakatar da yaki tsawon kwanaki uku

Isra´ila ta yi watsi da kiran da jami´in kula da taimakon jin kai na MDD Jan Egeland yayi na tsagaita wuta na tsawon sa´o´i 72 tsakanin Isra´ila da Hisbollah, don ba da damar kai agaji zuwa kudancin Libanon. Wani kakakin gwamnatin Isra´ila ya ce a tuni Isra´ila ta bude hanyoyin kai agaji a Libanon amma Hisbollah ce ke toshe wadannan hanyoyin don saka jama´a cikin wani mawuyacin hali. Bayan ya koma birnin New York daga yankin GTT mista Egeland ya fadawa kwamitin sulhun MDD cewa ya kamata a tsagaita wuta na tsawon kwanaki 3 a rikicin na Libanon. Yace wannan lokaci na da muhimmanci don kwashe wadanda suka yi rauni da kananan yara da kuma tsofaffi daga yankunan da ake batakashin a ciki.

“Ya ce zan sake komawa ga sassan wato isra´ila da Hisbollah, inda zan bukace su da su dakatar da kaiwa juna hare hare na stawon sa´o´i 72, don mu samu sukunin kwashe dubban jama´a da wannan rikici ya rutsa da su.”