Isra´ila ta yi lale da shirin kafa gwamnatin hadin kasa a Falasdinu | Labarai | DW | 12.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta yi lale da shirin kafa gwamnatin hadin kasa a Falasdinu

Isra´ila ta yi maraba da sanarwar da shugabannin Falasdinawa suka bayar ta kafa gwamnatin hadin kan kasa. A cikin wata sanarwa da ma´aikatar harkokin wajen Isra´ila ta bayar a birnin Kudus, ta ce wannan mataki zai ka iya taimakawa a sake farfado da shirin samar da zaman lafiya na yankin GTT. Da farko dai kungiyar Hamas mai matsanancin ra´ayi da kungiyar Fatah mai sassaucin ra´ayi sun ba da sanarwar cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa. An kai ga wannan mastayi ne baya an shafe watanni ana tattaunawa tsakanin shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da FM Isma´ila Haniyeh. To amma har yanzu Hamas ta ki sauraron kiraye kiraye na kasashen duniya na ta yi watsi da ayyukan tarzoma. Rahotanni sun ce nan da sa´o´i 48 masu zuwa za´a rushe gwamnati sannan a ba wa FM Haniyeh damar kafa sabuwar gwamnati.