Isra´ila ta yi barazanar hallaka Praministan Palestinu | Labarai | DW | 07.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta yi barazanar hallaka Praministan Palestinu

Ministan tsaron Isra´ila, Shaoul Mofaz , ya bayyana cewar saban pramistan palestinu, Ismael Haniyeh, na cikin haɗari zama gawa, muddun ƙungiyar Hamas, ta ci gaba, da kai hare haren ga yahudawa.

Wannan barazana, ta biwo bayan wata makamanciyar ta,da wani tsofan jami´in leƙen assirin Israela yayi jiya, inda ƙarara! ya hurta cewa, Ismael Haniyeh ya kussa zama mirganyi, muddun bai ɗauki mattakan wanzar da zaman lahia ba, tsakanin Israela da Palestinu.

Ƙungiyar Hamas, ba da wata wata ba,ta maida martnani, ga wannan kalamomi, da ta danganta da ta´adanci tsantsa.

Kakakin ƙungiyar, ya bayyana mamaki, a kan yada ƙasashe masu matsa ƙaimi ga Hamas, ba su ce uppan ba, ga wannan kalamomi.