1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ta yi barazanar daukar ƙarin matakan soji a Zirin Gaza

May 20, 2007
https://p.dw.com/p/BuL5

FM Isra´ila Ehud Olmert yayi barazanar daukar karin tsauraran matakan soji a Zirin Gaza idan Hamas ba ta daina kai harin rokoki cikin kudancin Isra´ila ba. Wani hari da Isra´ila ta kai ta sama a daren jiya yayi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 3. Akalla Falasdinawa 21 suka rasa rayukansu tun lokacin da jiragen saman yakin Isra´ila suka fara kai farmaki a Gaza kwanaki 5 da suka wuce. Ministan zamantakewa a Isra´ila Isakh Herzog ya baiyana halin da ake ciki a Gaza da cewa ba abin karbuwa ba ne ga Isra´ila saboda haka nan ba da dadewa ba zasu dauki karin matakan soji. Shi kuwa mai shiga tsakani a bangaren Falasdinu Saeb Erakat cewa yayi.

„Abin da ke faruwa yanzu a Gaza ba matsala ce da ta shafi Hamas o Fatah kadai ba. Matsala ce da ta shafi dukkan al´umar Falasdinawa. Saboda haka muna bukatar wata maslaha ta Falasdinu. Wannan maslaha kuwa ita ce maido da hukumomin Falasdinu.”