1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta turawa Falasdinawa kudaden haraji dala miliyan 118

Isra´ila ta turawa hukumar mulkin cin gashin kan Falasdinawa kashin farko na kudaden harajin ta da Isra´ila ta rike. Wani kakakin gwamnatin Falasdinu a birnin Ramallah na gabar Yamma da Kogin Jordan ya tabbatar da cewa an tura musu dala miliyan 118 zuwa ajiyar bankin hukumar mulkin Falasdinawa. Tun bayan da kungiyar Hamas ta lashe zaben gama gari da aka gudanar a yanukan Falasdinawa a farkon shekara ta 2006, Isra´ila ta dora hannu kan kudaden haraji da kwastan na hukumar mulkin Falasdinu. Kudaden kuwa sun kai dalar Amirka miliyan 400. A wani mataki na karfafa guiwar shugaban Falasdinawa mai sassaucin ra´ayi Mahmud Abbas, Isra´ila ta fara biyan kudaden kashi-kashi.