Israila ta tsagaita farmakin jiragen sama a Lebanon na saoí 48 | Labarai | DW | 31.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israila ta tsagaita farmakin jiragen sama a Lebanon na saoí 48

Israila ta sanar da tsagaita kai farmakin jiragen sama a kan Lebanon na saoí 48 daga ranar litinin din nan, sai dai kuma ta ce ta na da damar kai hari idan ta hakikance ana shirin kai mata farmaki. A luguden wuta da ta yi a ƙauyen Qana a ranar lahadi, ya hallaka mutane kusan 60 yawancin sun kananan yara. Wannan hari ya kassara ziyarar sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice a yankin gabas ta tsakiya a ƙarshen mako domin kawo ƙarshen faɗan tsakanin Israila da Hizbullah. Israilan ta ce zata gudanar da cikakken bincike a game da harin wanda ta ce kuskure ne.