1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila ta tsagaita farmakin jiragen sama a Lebanon na saoí 48

July 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuoV

Israila ta sanar da tsagaita kai farmakin jiragen sama a kan Lebanon na saoí 48 daga ranar litinin din nan, sai dai kuma ta ce ta na da damar kai hari idan ta hakikance ana shirin kai mata farmaki. A luguden wuta da ta yi a ƙauyen Qana a ranar lahadi, ya hallaka mutane kusan 60 yawancin sun kananan yara. Wannan hari ya kassara ziyarar sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice a yankin gabas ta tsakiya a ƙarshen mako domin kawo ƙarshen faɗan tsakanin Israila da Hizbullah. Israilan ta ce zata gudanar da cikakken bincike a game da harin wanda ta ce kuskure ne.