Isra’ila ta ba da sanarwar soke wata ziyarar da wani kwamiti, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta naɗa, don gudanad da bincike kan kisan gillan da ake zargin dakarunta da yi wa wasu Falasɗinawa 19 a gidansu a zirin Gaza a watan jiya. Wata kakakin majalisar ta ce Isra’ila ta ki amincewa da ziyarar kwamitin, wanda limamin limaman kiristan Afirka ta Kudun nan Archbishop Desmiond Tutu ke yi wa jagoranci.