Isra’ila ta shimfida ka’idojinta na ci gaba da hulda da Hukumar Falasdinawa. | Labarai | DW | 06.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra’ila ta shimfida ka’idojinta na ci gaba da hulda da Hukumar Falasdinawa.

Firamiyan rikon kwarya na Isra’ila, Ehud Olmert, ya ce kasarsa za ta ci gaba da hulda da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, muddin dai bai ba da hadin kai ga kungiyar Hamas ba. Kazalika kuma, ya ce wannan sharadin ne mizanin da gwamnatin Isra’ilan za ta yi aiki da shi wajen biyan kudaden shiga na haraji na wata-wata ga hukumar Falasdinawan. Muddin dai madafan iko ba su koma ga hannun kungiyar Hamas ba, to Isra’ila za ta ci gaba da biyan wadannan kudaden ga Hukumar Falasdinawan, inji shi.

Tun da Hamas ta lashe zaben Falasdinawan da aka gudanar cikin watan jiya ne, Isra’ila ta dakatad da biyan duk wasu kudaden haraji ga Hukumar Falasdinawan. A taron da ta yi jiya lahadi a birnin kudus ne, majalisar ministocin kasar bbani Yahudun, ta amince da biyan kimanin Euro miliyan 46 ga Falasddinawan. Wani shugaban kungiyar Hamas din ya ba da sanarwar cewa, kungiyar na fatar kafa Hukuma a cikin wannan watan, bayan da ta yarje da shugaba mai barin gado Mahmoud Abbas a kan ran 16 ga wannan watan watan, tamkar ranar da sabuwar Majalisar Falasdinun za ta yi zamanta na farko.