1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ta sake kai hari ta sama a Zirin Gaza

May 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuL2

Wani sabon hari da Isra´ila ta kai ta sama a arewacin Zirin Gaza ta halaka akalla Falasdinawa 4, dukkan su ´ya´yan kungiyar Jihadin Islami. Wata mai magana da yawon rundunar sojin Isra´ila ta tabbatar da kai wannan hari akan Falasdinawa dake ci-gaba da harba rokoki cikin Isra´ila. Ministan kula da tsaron cikin gida na Isra´ila, Avi Dichter yayi barazanar cewa zasu yi farautar shugaban Hamas dake gudun hijira a Syria, Khaled Mashaal don su yi masa kisan gilla. Ya ce Isra´ila ba zata bata lokaci ba wajen halaka Mashaal da zarar damar yin haka ta samu.