Isra´ila ta sake kai farmaki a kan filin jirgin saman Beirut | Labarai | DW | 14.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta sake kai farmaki a kan filin jirgin saman Beirut

Karo na 3 cikin sa´o´i 24 Isra´ila ta sake kai farmaki ta sama akan babban filin saukar jiragen saman birnin Beirut, wanda aka rufe shi bayan hari na farko da Isra´ila din ta kai a jiya. Da farko jiragen saman yakin Isra´ila sun kai hare hare a kudancin babban birnin na Lebanon, inda sojojin sa kai na Hezbollah ke da sansanoni. A yau jiragen saman yakin Isra´ila sun kai hari akan tashar samar da wutar lantarki da babbar hanyar da ke zuwa filin jirgin saman Beirut da kuma babbar hanyar da ta hada birnin da Damaskus babban birnin kasar Syria. Yanzu haka dai rahotanni sun ce mutane sama da 60 Isra´ila ta halaka a Lebanon yayin da rokokin da Hezbollah ke harbawa cikin arewacin Isra´ial suka yi sanadiyar mutuwar ´yan Isra´ila biyu.