Isra´ila ta rufe ofisoshin Hamas a gabashin Birnin Kudus | Labarai | DW | 15.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta rufe ofisoshin Hamas a gabashin Birnin Kudus

´Yan sandan Isra´ila sun rufe manyan ofisoshin yakin nema zabe na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas dake gabashin Birnin Kudus. Wani kakakin ´yan sandan ya ce an kame ´ya´yan kungiyar Hamas su 10 a samamen da aka kai yau lahadi. Daga cikin wadanda aka kaman akwai ´yan takara 3 wadanda aka zarga da yin kamfen ba bisa ka´ida ba. Hakan dai ya zo ne kasa da awa daya bayan da majalisar ministocin Isra´ila ta haramtawa kungiyar ta masu gwagwarmaya da makami yin takara a zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinu wanda zai gudana a ranar 25 ga wannan wata na janeru. A gun taron majalisar ministocin yau da safe, a hukumance Isra´ila ta amince larabawa mazauna gabashin Birnin Kudus su shiga zaben amma ta ce ba zata yarda kungiyar Hamas ta yi yakin neman zabe ba a wannan yanki da Isra´ila ta mayar da shi karkashin ikon ta.