Isra´ila ta lashi takobin ci-gaba da kai munanan hare hare akan Hisbollah | Labarai | DW | 25.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta lashi takobin ci-gaba da kai munanan hare hare akan Hisbollah

Duk da kokarin da ake na diplomasiya don yin sulhu cikin ruwan sanyi, Isra´ila ta jaddada cewar zata ci-gaba da daukar tsauraran matakan soji akan kungiyar Hisbollah a Libanon. Bayan ganawar da yayi da sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice yau a birnin Kudus FM Isra´ila Ehud Olmert ya ce kasar ta lashi takobin ci-gaba da yakin. Rice wadda ta jaddada bukatar cimma tsagaita wuta bisa wasu sharudda, ta ce lokaci yayi da za´a samar da abin da ta kira sabon yankin GTT. Ta ce dole ne a samu wani sulhu mai dorewa daga wannan gumurzu da ake yi tsakanin Isra´ila da Hisbollah.