Israila ta kashe Palasdinawa 18 a Beit Hanoun | Labarai | DW | 08.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israila ta kashe Palasdinawa 18 a Beit Hanoun

Sojojin Israila sun kashe akalla mutane 18 cikin wani hari da suka kai da safiyar yau laraba a arewacin Beit Hanoun.

Jamian kula da lafiya na Palasdinu sunce mutane 13 ne suka halaka da dama kuma suka samu rauni,dukkanin wadanda aka kashe mata ne da yara suna cikin barci.

Daruruwan jamaa da suka taru a bakin asibitin Kamal Adwan,suna masu zubda hawaye yayinda ake iso da gawarwakin yara da mata wasu cikin kayan barci.

Rundunar sojin Israila tun farko ta sanarda kashe wasu Palasdinawa 4 sojin sa kai da farar hula daya cikin wani hari data kai a Jenin,yamma da gabar kogin Jordan.

Jamian kula da lafiya na Palasdinu sunce wadanda aka kashen membobin kungiyar shahidan Alaqsa ne.

Tun farko dakarun sojin Israila sun kashe wasu mutane 7 cikinsu har da wata mace cikin hare hare da suka kai a yankuna 3 a arewacin Gaza.

Wadannan hare hare sun biyo bayan janyewar dakarun daga Beit Hanoun dake arewacin zirin Gaza,bayan mako guda na hare hare da Israilan ta kaddamar,wanda yayi sanadiyar mutuwar Palasdinawa kusan 50 da kuma sojan Israial daya.