Isra’ila ta kammala janye dakarunta daga Lebanon. | Labarai | DW | 01.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra’ila ta kammala janye dakarunta daga Lebanon.

Isra’ila ta ba da sanarwar cewa ta gama janye dakarunta daga kudancin Lebanon, kuma ta miƙa ragamar ikon yankin ga sojin Lebanon ɗin da kuma rundunar ƙasa da ƙasa ta kare zaman lafiya. Wannan matakin dai na ɗaya daga cikin ƙ’aidojin ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ya kawo ƙarshen yaƙin da Isra’ilan ta gwabza da Ƙungiyar Hizbullahi. Kafin dai cim yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar, wadda ta fara aiki a ran 14 ga watan Agusta, dakarun Isra’ila dubu 10 ne suka kutsa cikin yankunan kudancin Lebanon ɗin.

A wata sabuwa kuma, Isra’ilan ta ce tana auna yiwuwar faɗaɗa ɗaukin da sojinta ke yi a zirin Gaza, wai don hana Falasɗinawa ci gaba da harba mata rokoki. Babban hafsan hafsoshin sojin Isra’ilan, Manjo-Janar Dan Halutz, ya faɗa wa gidan rediyon ƙasar cewa, suna nan suna shawarwari kan yadda za su hana Falasɗinawa harba rokoki a kan garin Sderot, da ke kudancin Isra’ila, wanda kuma Falasɗinawan suka fi mai da shi abin bararsu.